logo

HAUSA

Rahoton MDD: Afrika na fuskantar karayar tattalin arziki mafi muni a shekaru 25 a lokacin annobar COVID-19

2021-03-03 11:02:12 CRI

Wani rahoton da hukumar kula da tattalin arzkin Afrika ta MDD, UNECA ta fitar ya nuna cewa, nahiyar Afrika tana fama da karayar tattalin arziki mafi muni da ba ta taba gani ba cikin shekaru 25 sakamakon tasirin barkewar annobar COVID-19.

Rahoton, mai taken “Mataki na gaba na gina Afrika domin samun farfadowa," wanda aka wallafa a ranar Litinin, ya bayyana karara game da dabarun farfado da tattalin arzikin nahiyar bayan kawo karshen annobar COVID-19.

Sakamakon binciken rahoton ya bayyana cewa, nahiyar Afrika ta tsunduma cikin yanayin karayar tattalin arzikin da ba ta taba ganin irinsa ba a shekaru 25, inda ta tafka hasarar da aka kiyasta ya kai dala biliyan 99 a sanadiyyar annobar COVID-19.

A cewar rahoton, tasirin annobar ya hada har da tasirin matsalar sauyin yanayi, inda suka karya tattalin arzikin lamarin ya janyo ake hasashen akwai yiwuwa nahiyar za ta iya hasarar GDPnta da kashi 3-4 nan da shekarar 2030.

Rahoton, ya yi nuni da kwararan matakan da suka dace nahiyar ta dauka domin farfadowa da kuma cimma nasarar muradin samar da dawwamamman cigaba na SDGs, da samun nasarar aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, da kuma ajandan bunkasa cigaban Afrika ta shekaru 50 nan da shekarar 2063.(Ahmad)