logo

HAUSA

AU ta bukaci kasashe mambobinta da su tabbatar da tsarin zabe mai kyau a lokacin annobar COVID-19

2021-03-03 09:47:28 CRI

Majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar Afrika AU ta bukaci kasashe mambobinta, wadanda ke shirin gudanar da zabuka a lokacin da ake fama da annobar COVID-19, da su tabbatar da yin tsari mai kyau karkashin ka’idojin AU.

A taronta na baya bayan nan, majalisar ta mayar da hankali kan zabukan da ake shiryawa a Afrika a tsakanin watan Yuli zuwa Disambar shekarar  2020 da kuma zabukan da za a gudanar a rubu’in farko na shekarar 2021, AU ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

Kasashen Afrika da suka hada da Burkina Faso, jamhuriyar tsakiyar Afrika, Kwadebuwa, Ghana, Guinea, Nijer, Tanzania da Uganda sun shirya zabukansu tsakanin watan Yuli zuwa Disamban 2020, yayin da kasashen Kongo da Somalia ake sa ran za su gudanar da nasu zabukan a rubu’in farko na shekarar ta 2021.

Majalisar ta jaddada muhimmancin da kasashen mambobinta ke da shi wanda hakan ya sa ta yanke kudirin tabbatar da ganin an shirya zabukan, ta yadda za a tabbatar da kiyaye lafiya da tsaron al’ummun kasashen daga kamuwa da annobar.(Ahmad)