logo

HAUSA

Sin: Ya kamata a sanya sabbin fasahohi su amfani jama’ar duniya

2021-03-03 20:25:41 CRI

Hukumar ’yancin mallakar kira ta duniya ta sanar a kwanan baya cewa, kasar Sin ta zama kan gaba a duniya a fannin yawan neman samun ’yancin mallakar kira a shekaru 2 a jere.

Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau Laraba cewa, lamarin ya nuna yadda kasar Sin ke ta samun ci gaba a fannin kirkiro sabbin fasahohi, da yadda jama’ar kasar ke fahimtar muhimmancin ’yancin mallakar kira da ilimi.

A sa’i daya kuma, kakakin Sin ya jaddada cewa, ya kamata a sanya sabbin fasahohin su amfani jama’ar kasashe daban daban, maimakon a boye su ba tare da yin amfani da su da kyau ba. (Bello Wang)

Bello