logo

HAUSA

Ko Akwai Abin Da Zai Ceci Amurka Daga “Cutar Wariyar Launin Fata”?

2021-03-03 10:51:54 CRI

Ko Akwai Abin Da Zai Ceci Amurka Daga “Cutar Wariyar Launin Fata”?_fororder_hoto

Cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, za a yanke hukunci kan wani dan sandan kasar Amurka da ya kashe bakar fatan nan George Floyd, ko da yake, a baya, Amurkawa a fadin kasar, sun nuna adawa kan wannan batu, amma, ba su iya canja halin da kasar take ciki ba.

Kasar Sin za ta gabatar da rahoton “keta hakkin bil Adama a kasar Amurka a shekarar 2020” a ‘yan kwanaki masu zuwa. A cikin wannan rahoto, an nuna cewa, adadin bakar fata da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka, ya ninka sau 3 idan aka kwatanta da adadin farar fata da suka kamu da cutar, kuma adadin bakar fata da suka rasu sakamakon cutar ya ninka sau biyu, idan aka kwatanta da adadin farar fata da suka rasa rayukansu sakamakon cutar a kasar Amurka. Kuma, a kan nuna ra’ayin wariyar launin fata ga ragowar al’ummomi na ketare dake zaune a cikin kasar Amurka.

Cikin tarihin kasar Amurka, an sha yin zanga-zanga, domin nuna adawa da ra’ayin nuna wariyar launin fata, amma, ra’ayin girman farar fata yana kara samun gindin zama a zaman takewar al’ummar kasar, wanda ya hana neman daidaito a tsakanin kabilu daban daban na kasar Amurka.

Abin bakin ciki shi ne, ‘yan siyasan kasar Amurka ba su son yin kome domin warware wannan matsala, inda wasu daga cikinsu, suke neman tsoma baki a harkokin gidan sauran kasashen duniya, bisa hujjar kare hakkin dan Adam.

Inda gwamnatin kasar Amurka ba ta dauki matakan da suka dace domin warware matsalar nuna wariyar launin fata da ake fama da ita a kasarta ba, to, maganar da Martin Luther King ya taba fadi cewar “Na yi mafarki”, to mafarki kawai zai tabbata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)