logo

HAUSA

WIPO: Takardun bukatar mallakar fasaha a duniya na ci gaba da karuwa duk da annobar COVID-19

2021-03-03 09:05:47 CRI

Wani rahoto da kungiyar kare ‘yancin mallakar fasaha ta duniya ta fitar, ya nuna cewa, takardun bukatar mallakar fasaha da aka gabatar a duniya ta hannun kungiyar a shekarar 2020, sun ci gaba da karuwa, duk da annobar COVID-19 da ke addabar sassan duniya.

Rahoton ya ce a shekarar 2020, takardun bukatar da aka gabatar ta hannun tsarin yarjejeniyar kungiyar (PCT), daya daga cikin ma’aunin da ake amfani da shi wajen kimanta ayyukan kirkire-kirkire, sun kai 275,900, karuwar kaso 4 cikin 100, kana adadin mafi yawa da aka taba samu, duk da raguwar GDPn kasashen duniya da aka yi kiyasi na kaso 3.5.

A shekarar 2020, kasar Sin ta gabatar da takardun bukatar mallakar fasaha 68,720, ko karuwar kaso 16.1 kan na shekarar da ta gabace ta, kasar dake kan gaba wajen cin gajiyar tsarin yarjejeniyar kungiyar(PCT).

Shekaru hudu ke nan a jere, kamfanin fasahar sadarwa na Huawei na kasar Sin, ya ke kasancewa a kan gaba, inda ya wallafa takardun bukatu 5,464 karkashin tsarin yarjejeniyar hukumar, abin da ya sanya kamfanin zama a kan gaba wajen gabatar da takardun bukata a shekarar ta 2020.(Ibrahim)