logo

HAUSA

Guo Weimin: Yiwa rigakafin da Sin ke fitarwa ketare wani kallo maras kyau rashin hangen nesa ne

2021-03-03 20:53:41 CRI

Guo Weimin: Yiwa rigakafin da Sin ke fitarwa ketare wani kallo maras kyau rashin hangen nesa ne_fororder_0303-allura-Saminu-hoto

Kakakin majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC Mr. Guo Weimin, ya ce wadanda ke kallon kokarin da Sin ke yi, na samarwa kasashe daban daban rigakafin cutar COVID-19, a matsayin hanyar fadada tasirin siyasa, ba su da hangen nesa.

Guo, wanda ya yi wannan tsokaci yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Larabar nan, ya ce tuni kasar Sin ta ayyana rigakafin da take samarwa, a matsayin wata haja ga duniya baki daya, kuma gwamnatin kasar na karfafa gwiwar kamfanonin dake samar da rigakafin a cikin kasar, da su yi hadin gwiwa da cibiyoyin binciken rigakafi na kasashe daban daban, don ci gaba da kirkira, da kuma samar da isassun rigakafin.

Jami’in ya kara da cewa, har kullum Sin na sanya inganci, da tasirin rigakafin COVID-19 na kasar gaban komai. Tuni kuma nau’oi rigakafin na Sin suka samu amincewa, aka kuma fara amfani da su a cikin kasar, da ma sauran kasashe daban daban, har wasu shugabannin kasashe ma na shiga gaba, wajen fara karbar rigakafin na Sin.  (Saminu)