logo

HAUSA

Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta karyata zargin da aka yi wa kasar

2021-03-03 19:42:44 CRI

Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta karyata zargin da aka yi wa kasar_fororder_hakki

Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin, ta mika wasu rahotonni guda 5 ga zama na 46, na kwamitin lura da hakkin dan Adam na MDD a kwanan baya, inda a cikin su ta bayyana yanayin da ake ciki game da kare hakkin dan Adam a kasar Sin, musamman ma a fannonin dakile cutar COVID-19, da kawar da talauci a jihar Tibet, da raya jihar Xinjiang, tare da karyata zargin da wasu kasashen dake yammacin duniya suka yi wa kasar ta Sin.

An bayyana cewa, yayin da kasar Sin ke kokarin tinkarar cutar COVID-19, tana mai da rayuka da lafiyar jikin jama’ar kasar a gaban komai, tare da kokarin tabbatar da hakkinsu a dukkan fannoni. Kana a jihar Tibet ta kasar, an dauki wasu matakai, irinsu sauya matsuguni ga mutane marasa karfi, da raya wasu sana’o’i, da ba da tallafi ga mutane masu bukata, tare da cimma manyan nasarori.

Game da karyar da aka jinginawa kasar Sin, cewa wai tana muzgunawa ‘yan kabilar Uygur, alkaluman da aka samu sun shaida cewa, yawan al’ummar kabilar Uygur na ta karuwa, cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce. Don haka masu yiwa Sin kazafin cewa tana aiwatar da matakan rage yawan al’ummar kabilar Uygur, suna yi ne domin neman bata sunan kasar.

Kana kamfanonin kasar Sin ba su taba tilastawa wani ya yi aiki, ko kuma sanyawa mutane ido ba. Ko shakka babu, ana tabbatar da hakkin aiki na al’ummun kabilu daban daban, na jihar Xinjiang yadda ya kamata. (Bello Wang)

Bello