logo

HAUSA

CAAC:Bangaren zirgar-zirgar jiragen saman kasar Sin yana bunkasa

2021-03-03 09:59:13 CRI

Hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama na kasar Sin sun bayyana cewa, sashen zirga-zirgar jiragen saman kasar, ya bunkasa a ‘yan shekarun nan. Ya zuwa karshen shekarar 2020, yawan jiragen sama a kasar sun karu zuwa 2,844.

Alkaluman kididdiga da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin (CAAC) ta fitar, sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, yawan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama a kasar, sun karu zuwa 523.

A cewar hukumar ta CAAC, baya ga samun ci gaba mai dorewa a fannin harkokin kasuwanci na yau da kullum da jirage, bangaren zirga-zirgar jiragen saman kasar, shi ma ya samu ci gaba a sabbin fannoni na kasuwanci.

Haka kuma, ya zuwa karshen shekarar 2020, yawan jirage masu sarrafa kansa da aka yiwa rijista a kasar Sin, sun kai 523,000, inda suka yi tafiye-tafiye na sa’o’i fiye da miliyan 1.59 a shekara.

Alkaluma da hukumar ta CAAC ta fitar na nuna cewa, bangaren zirga-zirgar jiragen saman kasar, ya samu bunkasuwa a fannin kallon wuraren shakatawa ta sama da laimar sauka daga sama. Ya zuwa karshen shekarar 2020 da ta gabata, akwai sama da hanyoyin zirga-zirgar wuraren shakatawa ta sama fiye da 100, inda ya samar da hidimomi na shakatawa ta sama ga wuraren yawon bude ido kimanin 50 a fadin kasar baki daya.(Ibrahim)