logo

HAUSA

An cimma burika 17 da aka tsara cikin rahoton aikin gwamnati a shekarar 2020

2021-03-03 13:39:59 CRI

Jiya Talata, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, an cimma burika guda 17 da aka tsara cikin rahoton aiki na gwamnati na shekarar 2020, kuma an kammala wasu ayyuka daga cikinsu fiye da yadda ake fata.

Da farko, an kammala ayyuka masu nasaba da zaman rayuwar al’umma da kyau. Kamar burin samar da karin guraben ayyukan yi miliyan 9 a birane da garuruwa, gaba daya, an samar da karin guraben ayyukan yi miliyan 11.86 a birane da garuruwan kasar Sin. Kuma, a fannin burin daidaita karuwar farashin kayayyakin yau da kullum cikin 3.5%, adadin karuwar farashin kayayyakin yau da kullum bai wuce 2.5% ba. Sa’an nan, a shekarar 2020, an kuma cimma burin ba da horo kan fasahohi da daukar dalibai a makarantun koyon sana’o’i, bisa shirin kasar Sin na ba da horo ga mutane sama da miliyan 35, da kuma kara daukar dalibai kimanin miliyan 2 a makaratun koyon sana’o’i cikin shekaru biyu, wato shekarar 2020 da shekarar 2021.

Bugu da kari, an cimma sakamako mai gamsarwa a fannin rage kudaden da kamfanoni suka kashe wajen gudanar da ayyukansu, inda a shekarar 2020, gaba daya, kamfanonin kasar sun ajiye kudin da ya kai sama da RMB yuan triliyan 2.5.

Al’ummomin kasar Sin sun gamsu kwarai da gaske, game da yadda aka cimma nasarorin kyautata manufofin yin kwaskwarima da kuma kammala ayyuka masu nasaba da zaman rayuwar al’umma. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)