logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya bukaci a kara sanya ido bayan sakin dalibai matan da aka sace

2021-03-03 11:08:47 CRI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci al’umma da ta sanya ido sosai, a wani mataki na tattara isassun bayanan sirri a kan lokaci, ta yadda za a dakile gungun bata garin dake addabar jama’a.

Buhari ya yi wannan kira ne, bayan samun rahoton sakin dalibai mata da aka sace a makarantar sakandaren kimiya ta gwamnati (GGSS) a garin Jangebe na karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara dake yankin arewa maso yammacin kasar jiya da safe.

Shugaban ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan matsala ta sace-sacen mutane a kasar baki daya.

A don haka, ya yi gargadi jama’a da su daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa, yin haka a cewarsa, ba zai kawo karshen matsalar ba. Ya kuma bukaci ‘yan sanda da sojoji, da su zakulo ‘yan fashin domin su fuskanci shari’a.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, jihar da aka sace daliban, ya bayyana cewa, an saci yaran ne, ta hanyar sasantawa. Ya kuma hakikance cewa, babu wani kudin fansa da aka biya ‘yan fashin kafin su saki daliban, kuma sakin daliban, sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyar da ya bullo da ita ne.(Ibrahim)