logo

HAUSA

Wakilin Sin dake MDD ya yi bayani kan fasahohin Sin na yaki da talauci

2021-03-03 16:13:52 CRI

Wakilin Sin dake MDD ya yi bayani kan fasahohin Sin na yaki da talauci_fororder_210303-bayani-maryam2-hoto

Jiya Talata, wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya yi wa kasashe mambobin MDD da ofishin sakataren MDD, da wasu hukumomin da abin ya shafa da kuma kafofin watsa labarai na kasar Sin da na kasashen ketare bayani kan fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su wajen yaki da talauci da kuma sakamakon da kasar ta cimma. Haka kuma Zhang Jun ya yi irin wannan bayani a taron manema labaran da aka kira ta kafar bidiyo mai taken “Aiwatar da ajandar neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030: fasahohin kasar Sin na kawar da talauci”.

A yayin taron, Zhang Jun ya bayyana cewa, nasarar da kasar Sin ta cimma wajen kawar da talauci, tana da muhimmiyar ma’ana ga bunkasuwar kasar Sin da ma dukkanin kasashen duniya a nan gaba, inda ya tattauna da wakilan bangarori daban daban game da fasahohin kasar Sin na kawar da talauci.

Bangarorin da abin ya shafa sun taya kasar Sin murnar cimma nasarar kawar da talauci, suna ganin cewa, nasarar da Sin ta cimma ta janyo hankulan kasa da kasa. Haka kuma kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ga kasashen duniya wajen aiwatar da ajandar MDD game da neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030. (Mai Fassara: Maryam Yang)