logo

HAUSA

Sin za ta samar da tallafin alluran riga-kafin cutar COVID-19 karo na biyu ga kasar Masar

2021-03-03 14:15:20 CRI

Sin za ta samar da tallafin alluran riga-kafin cutar COVID-19 karo na biyu ga kasar Masar_fororder_1

A wajen wani taron manema labarai da aka shirya kwanan nan a birnin Alkahira, jakadan kasar Sin dake kasar Masar, Liao Liqiang ya sanar da cewa, gwamnatin Sin za ta samar da tallafin alluran riga-kafin cutar COVID-19 kashi na biyu ga Masar, a wani mataki na marawa al’ummar kasar baya wajen dakile cutar gami da farfado da ayyukansu yadda ya kamata.

Jakada Liao ya bayyana cewa, a ranar 22 ga watan Fabrairun bana, shugaba Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Masar Abdelfattah al Sisi ta waya, inda suka cimma matsaya daya kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi karfafa hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin yaki da yaduwar cutar. Kashegari, kashin farko na alluran riga-kafin cutar da kasar Sin ta tallafa suka isa Alkahira. Yanzu kuma, Liao Liqiang ya ce kasarsa za ta kara taimakawa Masar:

“Akwai wani albishiri da zan sanar muku. Gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar samar da kashi na biyu na alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kamfanin Sinopharm ya samar ga Masar. Ta hanyar irin wannan kokari, muna fatan goyon-bayan matakan da al’ummar Masar suke dauka na ganin bayan cutar, da farfado da harkokin su na yau da kullum. Kasar Sin na son raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tare da Masar a fannin lafiyar dan Adam.”

Jakada Liao ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin tana kuma goyon-bayan kamfanoninta su sayar wa Masar alluran riga-kafin bisa bukatun ta, tana kuma goyon-bayan kamfanoninta su hada kai tare da kamfanonin Masar a fannin samar da alluran riga kafin.

Game da gudummawar da alluran riga-kafin na kasar Sin suke bayarwa ga fadin duniya, jakada Liao ya ce, zama tsintsiya madaurinki daya wajen dakile cutar, na da matukar muhimmanci ga aikin taka birki ga yaduwar cutar, kuma alluran riga-kafin tamkar muhimmin makami ne na yakin da ake yi. Idan kasashe masu tasowa ba su shiga aikin dakile cutar ba, ba za a samu hadin-gwiwar kasa da kasa yadda ya kamata ba. Jakada Liao ya ce:

“Idan kasashe masu tasowa ba su iya samun isassun alluran riga-kafin cutar ba, da kyar a samu cikakkiyar nasara wajen ganin bayan cutar a duk duniya. Yawan al’ummomin kasar Sin ya kai biliyan 1.4, duk da cewa suna bukatar alluran riga-kafin sosai da sosai, amma kasar Sin tana iyakacin kokarinta wajen hada kai tare da sauran kasashe, da himmatuwa wajen samar da tallafin alluran riga-kafin ga kasashe masu tasowa.”

Jakada Liao ya jaddada cewa, kamar abun da memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya fada a wajen taron ministoci kan batun yaki da COVID-19 da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya shirya, Sin tana kokarin hada kai da sauran kasashe a fannin samar da alluran riga-kafin, ba tare da gindaya wani sharadi na siyasa, ko neman samun moriyar tattalin arziki ba. Abun da kasar Sin take lura shi ne, alluran riga-kafin za su zama wani kayan amfanin al’ummomin kasashe daban-daban wadanda kowa zai iya saya cikin sauki da kuma araha.

Game da batun yiwa Sinawa dake kasar Masar alluran riga-kafin cutar, jakada Liao ya ce, ofishin jakadancin Sin dake Masar yana mu’amala sosai da ma’aikatar lafiya ta Masar, domin yiwa alluran riga-kafin ga Sinawa dake kasar ba tare da bata lokaci ba, kuma bisa tushen girmama dokokin Masar da muradun Sinawan. Jakada Liao ya ce:

“Sanin kowa ne cewa, tun bayan barkewar cutar, jam’iyyar kwaminis gami da gwamnatin kasar Sin suna maida hankali sosai kan halin da Sinawa dake kasashen waje suke ciki. Ofishin jakadancinmu shi ma yana kokarin mu’amala da ma’aikatar lafiyar Masar, don Sinawa dake kasar su karbi alluran ba tare da bata lokaci ba. Manyan jami’an ma’aikatar lafiya ta Masar sun bayyana cewa, Sin da Masar aminan juna ne na musamman, kana Masar za ta nuna kwazo wajen taimakawa Sinawa dake kasar samun alluran riga-kafin cutar.”

Liao ya kuma ce, ofishin jakadancin Sin dake Masar yana fatan ci gaba da himmatuwa wajen taimakawa Sinawa dake wajen daukar matakan kandagarkin cutar.(Murtala Zhang)