logo

HAUSA

Majalissar CPPCC ta kasar Sin za ta gudanar da taron ta tsakanin ranekun 4 zuwa 10 ga watan nan

2021-03-03 19:13:58 CRI

Majalissar CPPCC ta kasar Sin za ta gudanar da taron ta tsakanin ranekun 4 zuwa 10 ga watan nan_fororder_7227692661910219906

Majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC a takaice, za ta gudanar da taronta na shekara-shekara na bana, tsakanin ranekun 4 zuwa 10 ga watan nan na Maris.

Kakakin majalissar Guo Weimin, ya shaidawa taron manema labarai da ya gudana a yau cewa, majalissar ta 13, za ta kaddamar da zaman nata na 4 ne, da yammacin gobe Alhamis. Guo ya kara da cewa, an tsara gudanar da zaman zauren majalissar guda biyu, da kuma wasu tarukan na rukunoni guda 6. Kaza lika za a yi zaman zauren majalissar guda 1 ne ta kafar bidiyo.

Daga nan sai jami’in ya tabbatar da kammala dukkanin shirye shiryen da aka tsara, domin gudanar da taron cikin nasara.  (Saminu)