logo

HAUSA

Sin: Zumuntar dake tsakanin jama’ar Sin da Amurka za ta taimakawa raya huldar kasashen 2

2021-03-03 19:55:21 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya furta a yau Laraba cewa, zumuntar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, ita ce tushen raya huldar dake tsakanin kasashen 2. To sai dai kuma, yadda tsohuwar gwamnatin kasar Amurka, da wasu mutane masu kin jinin kasar Sin suka yi kokarin shafawa kasar Sin kashin kaji, ya haifar da mummunan tasiri ga ra’ayin jama’ar kasashen 2.

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kamfanin Gallup ya yi, ya nuna cewa, yanzu haka Amurkawa ba su amince da kasar Sin sosai ba. Dangane da hakan, Wang ya ce an gabatar da rahotonni daban daban, game da huldar dake tsakanin Sin da Amuka, inda a cikin wasunsu, aka nuna yadda ya kamata a karfafa cudanyar Sin da Amurka a fannin al’adu. A daya banagaren kuma, akwai kashi 72% na Amurkawa da aka yi binciken ra’ayinsu, da suka yarda da hadin gwiwa da kasar Sin, a fannin tinkarar batun sauyin yanayi.

Ban da wannan kuma, Wang ya ce kasar Sin na cikin damuwa, bisa yadda ake ta samun batutuwan nuna bambanci ga ’yan asalin kasashen Asiya, ciki har da Sinawa, wadanda ke zaune a kasar Australiya. (Bello Wang)

Bello