logo

HAUSA

Najeriya ta karbi riga-kafin COVID-19 miliyan 3.94 da ta jima tana tsammaninsa

2021-03-03 10:19:09 CRI

A jiya Talata Najeriya ta karbi kashin farko na alluran riga-kafin annobar COVID-19 guda miliyan 3.94, wanda kasar ta jima tana dakon zuwansa karkashin shirin tallafawa kasashen duniya na COVAX, mai taimakawa shugaban kasar ne ya bayyana hakan a Abuja.
Bayan karbar alluran, Najeriya ta zamanto kasa ta uku daga yammacin Afrika da ta karbi riga-kafin na shirin COVAX baya ga kasashen Ghana da Kwadebuwa.
Wannan shi ne rukunin farko na muhimman kayan aikin da Najeriyar take tsammanin zuwansa a kokarin dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar.
A wata sanarwar da ofishin MDD dake Najeriya ya fitar, ya ce isowar alluran wani muhimmin al’amari ne mai cike da tarihi karkashin shirin tabbatar da yin raba daidai na riga-kafin annobar COVID-19 a tsakanin kasashen duniya.
Karamin ministan lafiyar Najeriya Olorunimbe Mamora ya bayyana cewa, hukumomin Najeriya sun sha alwashin gudanar da riga-kafin cutar ta COVID-19 a matakai daban daban, da rarraba shi bisa adalci, da kuma tabbatar da yiwa dukkan al’ummar Najeriya da suka cancanci samun riga-kafin nan da shekaru biyu masu zuwa.
A cewar Mamora, dukkan shirye shirye sun kammala domin tabbatar da samun nasarar gudanar da riga-kafin a kasar. Ya ce daga cikin tsare tsaren da aka yi har da baiwa ma’aikatan lafiyar kasar horo, da tanadar ingantattun wurare masu sanyi don adana alluran da kuma tsara yadda za a rarraba riga-kafin a dukkan unguwannin dake fadin kasar. (Ahmad)