logo

HAUSA

UNECA:Adadin masu fama da kangin talauci a Afirka zai karu zuwa miliyan 514 a wannan shekara

2021-03-04 10:38:14 CRI

Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin nahiyar Afirka (UNECA) ta yi gargadin cewa, muddin mahukuntan nahiyar Afirka ba su magance tasirin annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya ba, hakan ka iya kara ta’azza matsalar kangin talauci, inda ake hasashen ‘yan Afirka da yawansu ya kai mutum miliyan 514, suna iya fadawa mizanin kangin talauci a shekarar 2021 da muke ciki.

Hukumar UNECA ta yi gargadin cewa, idan har nahiyar Afirka ba ta samu ci gaba cikin hanzari a shekarun dake tafe fiye da wanda ta samu kafin annobar COVID-19 ba, hakika hasashen da aka yi game da ci gaba a nahiyar gami da tasirin annobar COVID-19, za su ci gaba da sanya shakku game da kokarin kasashen na cimma wannan buri.

A cewar hukumar, tasirin matsalar sauyin yanayi, shi ma wani babban kalubale ne ga tattalin arzikin kasashen na Afirka, kari kan tasirin annobar COVID-19.

Sai dai kuma, duk da ci gaban da kasashen nahiyar ta Afirka suka samu wajen rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, da kara wani adadi na muhimman yankunan rabe-raben halittu da kaso 4.6 cikin 100 tsakanin shekarar 2010 da 2020, a hannu guda kuma, nahiyar tana ci gaba da fuskantar matsalar sauyin yanayi, saboda karancin dabarun magance matsalar.(Ibrahim)