logo

HAUSA

Kwararre dan kasar Jamus na fatan Sin za ta fitar da sabbin dabarun warware kalubalen kasa da kasa cikin taruka biyu

2021-03-04 10:35:49 CRI

Wani kwararre a fannin nazarin harkokin Sin daga kasar Jamus, Wolfram Adolphi, ya ce, yana sa ran gudanar da manyan taruka biyu na kasar Sin. Kuma a ganinsa, kasar Sin ce kasa mafi yawan al’umma a duk fadin duniya, wadda ta sami gaggarumin ci gaba a fannin tattalin arziki cikin shekaru da dama da suka gabata, inda a yanzu, take da muhimmin tasiri ga kasa da kasa.

Wolfram Adolphi ya taba aikin nazari a hukumar nazari ta majalisar wakilan tarayyar Jamus, kuma dan jarida ne dake zaune a ketare, haka kuma, ya taba rubata littattafai da dama game da kasar Sin.

A cewarsa, a halin yanzu, kasashen duniya na fuskantar kalubale da dama dake shafar tattalin arziki, kuma, sauyin yanayi na barazana ga zaman rayuwar al’umma cikin kasa da kasa. A sa’i daya kuma, ana fuskantar babban kalubalen bunkasuwar harkokin yanar gizo. Shi ya sa, yake fatan kasar Sin za ta fitar da sabbin dabarun warware wadannan kalubale dake gaban kasa da kasa cikin manyan taruka biyu na wannan karo.

Yana mai cewa, “A ganina, abu mafi muhimmanci shi ne yadda kasar Sin take son ba da gudummawar warware kalubalen dake jan hankulan kasa da kasa, na san Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin tana son kara hadin gwiwar kasa da kasa da shimfida zaman lumana a duk fadin duniya, kuma tana dukufa wajen karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen neman ci gaba da warware matsaloli tare. Shi ya sa, nake goyon bayan kasar Sin game da sabon shirin raya kasa cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma ina fatan za a aiwatar da shirin kamar yadda ake fata.” (Maryam)