logo

HAUSA

Masana a taron karawa juna sani sun tattauna batun aikin yi da ‘yancin kwadago a Xinjiang

2021-03-04 13:55:23 CRI

A jiya ne aka shirya taron karawa juna sani, game da batun aikin yi, da ‘yancin ‘yan kwadago a yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa ta kafar bidiyo, a gyefen zaman hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD karo na 46.

Mahalarta taron, sun mayar da hankali tare da musayar ra’ayoyi, kan matakan da mahukuntan yankin suke dauka, na kare ‘yancin aikin yi da ‘yan kwadago na dukkan kungiyoyin kananan kabilu, da kwarewar da yankin ya samu wajen taimakawa dukkan kananan kabilu dake yankin samun makoma mai kyau, ta hanyar samun aikin yi, baya yadda ci gaba da kare ‘yancinsu na samun ci gaba.

Masanan sun kuma amince cewa, manufofi da matakan da yankin ya dauka game da aikin yi, da tsaron guraben aikin yi, sun dace da dokoki da kundin tsarin mulkin kasar Sin, sun kuma dace da mizanin aikin yi na kasa da kasa, da kare hakkin dan-Adam. Sun kuma shimfida wani harsashi na kare ‘yancin rayuwa da ci gaban dukkan kungiyoyn kananan kabilu, baya ga samar da daidaito da adalci a tsarin jin dadin jama’a. (Ibrahim)