logo

HAUSA

Xi zai tattauna harkokin kasa da mambobin CPPCC

2021-03-04 10:42:15 CRI

Yau Alhamis 4 ga wata, za a kaddamar da taro na hudu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a takaice na 13 a nan birnin Beijing, inda shugaban kolin kasar Xi Jinping zai tattauna da mambobin majalisar, kan yadda za su tafiyar da harkokin kasa

Ga karin bayanin da abokiyar aikinmu Jamila ta hada mana.

A yayin babban taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da aka shirya a ‘yan shekarun da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha tattauna batutuwan da suka shafi harkokin kasa da mambobin majalisar, lamarin da ya nuna cewa, shugaba Xi ya yaba da rawar da majalisar take takawa, haka kuma ya nuna cewa, tsarin hadin gwiwar dake tsakanin jam’iyyu daban daban mai hallayar musamman ta kasar Sin da tsarin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar sun samu karbuwa matuka daga wajen al’ummun kasar ta Sin.

Shugaba Xi ya taba bayyana cewa,“Tsarin hadin gwiwar dake tsakanin jam’iyyu daban daban mai hallayar musamman ta kasar Sin da tsarin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar, shi ne tsarin siyasa mafi muhimmanci na kasar Sin, kana babban tsarin siyasa da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da al’ummun Sinawa da jam’iyyun demokuradiya da al’ummun kasa da ba na ‘yan jam’iyyu ba suka kafa, ana iya cewa, shi ne sabon tsarin jam’iyyu da aka kafa a kasar Sin.”

Yayin taruka biyu wato babban taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da babban taron ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar da aka shirya a shekarar 2018, a karo na farko babban sakataren JKS Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin sabon tsarin jam’iyyu, wanda ya jawo hankalin al’ummun kasa da kasa.

Shin, ya ya za a fahimci wani abu sabo daga tsarin jam’iyyun? Hakika ana iya fahimtar wani abu sabo daga ka’idarsa ta mayar da moriyar al’ummun kasa da farko, a maimakon wakilcin moriyar rukunoni kalilan, kuma ana iya fahimtar wani abu sabo daga matakin da aka dauka na hada kan jam’iyyu daban daban na kasar da al’ummun kasa da ba na ‘yan jam’iyyu ba, ta yadda za su hada kai tare domin cimma burin da aka tsara.

Babban sakatare Xi Jinping ya sha yin tsokaci cewa, yana fatan jam’iyyun demokuradiya daban daban da mutane da ba ‘yan jam’iyyu ba, ba za su manta da burinsu na gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu, a matsayinsu na masu ba da shawara da masu ba da taimako da kuma abokan aiki na gari na JKS, tare kuma da gudanar da harkokin kasar Sin yadda ya kamata, inda Xi ya bayyana cewa,“Ya dace a yi amfani da tsarin demokuradiyar nan na ba da shawara kan harkokin siyasa a nan kasar Sin, ta hanyar yin tattaunawa, ta haka za a cimma matsaya guda kan harkokin kasa, tare kuma da gudanar da harkokin kasa lami lafiya.”

Yayin tataunawar da ya yi da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa a babban taron majalisar da aka shirya a shekarar 2016, Xi ta taba bayyana ra’ayinsa kan huldar dake tsakanin siyasa da kasuwanci, yana mai cewa,“Kamata ya yi jami’an gwamnati su nuna sahihanci yayin da suke hulda da kamfanoni masu zaman kansu, haka kuma su daidaita matsalolin da suke fuskanta, bai dace ba su karbi kudi daga kamfanonin, kana ya kamata kamfanoni masu zaman kansu su gudanar da harkokinsu bisa doka.”

A yayin babban taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na shekarar 2017, Xi ya tattauna da mambobin da suka fito daga bangarorin al’adu da ba da ilmi da kiwon lafiya da kimiyya da fasaha, inda ya yi kira cewa, akwai bukatar masanan kasar Sin su kara ba da gudummowa kan farfadowar al’ummun kasar, da wadatar kasa, da kuma jin dadin rayuwar al’ummun Sinawa, a cewarsa:“Ya dace a kara mai da hankali kan moriyar kasa, da bunkasa ci gaban tattalin arziki, da tabbatar da tsaron kasa, ta hanyar yin kirkire-kirkire.”

Hakazalika, Xi ya jaddada cewa, ya kamata a sa kaimi kan cudanyar tunani daban daban, yana mai cewa,“Raya demokuradiyar tattaunawa mai salon tsarin gurguzu, ta hanyar mutunta juna, da yin hakuri ga juna, ta yadda za a bayyana ra’ayoyi kamar yadda suke so bisa ka’ida.”(Jamila)