logo

HAUSA

MDD:Masu aikin samar da agaji sun kasa kaiwa ga sama da mutane 76,000 da suka rasa muhallansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya

2021-03-04 10:07:57 CRI

Hukumar samar da agajin jin kai ta MDD (OCHA) da sauran abokan hulda, sun kasa kaiwa ga wuraren da sama da mutane 76,000 da suka rasa matsugunansu ke zaune a garin Dikwan jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

OCHA ta sanar da cewa, kimanin mutane 3,400 ne suka bar muhallansu, ciki har da sama da kananan 2,000, inda suke samun mafaka a garin Dikwa na jihar Borno, biyo bayan yawaitar hare-haren da kungiyoyin ‘yan bindiga ke kaiwa yankin Marte da kewaye, tun ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata, lamarin da ya kai ga karuwar mutanen da ke rasa muhallansu. An yi kiyasin cewa, akwai sama da mutane 76,000 da suka kauracewa muhallansu a garin na Dikwa, sakamakon tashin hankalin dake faruwa a yankin tun shekarar 2009.

Hukumar ta OCHA ta ce, hare-haren ranar 18 ga watan Fabrairu da na 1 ga watan Maris da aka kai yankin, sun kara takawa masu aikin jin kai birki, a kokarin da suke yi na isa wuraren, baya ga karuwar barazanar tsaro.

Jami’in tsare-tsare na MDD Edward Kallon, ya bayyana a ranar Talata cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ma, kungiyoyi masu dauke da makamai, sun kai hari kan cibiyoyin samar da agaji da dama a garin na Dikwa, ciki har da wani asibiti da aka ba da rahoton an cimma masa wuta.

MDD dai, ta sha yin kira ga dukkan kungiyoyin dake dauke da makamai, da su gaggauta dakatar da tayar da hankali, a tabbatar da kare rayukan fararen hula, da kayayyakin more rayuwar jama’a, da na agaji da ma’aikatansu.(Ibrahim)