logo

HAUSA

Tallafin allurar rigakafin COVID-19 da Sin ta baiwa Guinea sun isa kasar

2021-03-04 14:07:11 CRI

Tallafin allurar rigakafin COVID-19 da Sin ta baiwa Guinea sun isa kasar_fororder_hoto2

A jiya Laraba, tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Guinea, suka isa birnin Conakry fadar mulkin kasar. Jakadan kasar Sin dake kasar Guinea Huang Wei, da ministan harkokin wajen kasar Guinea Ibrahima Khalil Kaba, da ministan kiwon lafiyar kasar Guinea Remy Lamah da wasu jami’an kasar sun halarci bikin mika allura da aka shirya a filin jiragen sama.

Jakadan kasar Sin dake kasar Guinea Huang Wei ya bayyana cewa, yanzu babu isassun allurar rigakafin cutar COVID-19 a duniya, a yayin da kasar Sin take dukufa wajen biyan bukatun al’ummominta, tana kuma yin iyakacin kokarinta wajen samar da tallafin allurar rigakafin COVID-19 ga kasashe masu tasowa. Wannan shi ne matakin da kasar Sin ta dauka domin cika alkawarin da shugaban kasar Xi Jinping ya yi wa kasashen duniya, cewar, allurar rigakafi da Sin ta samar, za su kasance hajar al’ummomin duniya baki daya. Wannan mataki ya kuma nuna fatan kasar Sin na karfafa dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasar Guinea, da kuma taimaka wa al’ummomin kasar Guinea wajen cimma nasarar yaki da cutar cikin sauri.

A nasa bangare, ministan kasar Guinea Ibrahima Khalil Kaba ya nuna godiya matuka ga shugaba Xi Jinping, da gwamnati da kuma al’ummomin kasar Sin, a madadin shugaba, da gwamnati, da al’ummomin kasarsa. Ya kuma bayyana cewa, tabbas kasar Guinea za ta yi nasarar yaki da cutar bisa taimakon da kasar Sin ta samar mata. (Maryam)