logo

HAUSA

MDD na taimakawa wajen tura riga kafin COVID-19 zuwa Afrika

2021-03-04 10:02:36 CRI

MDD ta kai miliyoyin alluran riga kafin COVID-19 zuwa Afrika, ta hannun shirin COVAX na kawancen kasashe dake da nufin samarwa da raba riga kafin COVID-19 ga kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga.

Kakakin Sakatare Janar na MDD Stephane Dujarric, ya ce yanzu haka, alluran riga kafi sun isa kasashen Angola da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Gambia da Kenya da Rwanda da kuma Senegal.

Sama da allurai miliyan 1 ne asusun kula da yara na MDD ya kai kasar Kenya a jiya Laraba.

Kasar Rwanda kuwa ta karbi allurai 340,000, inda wakilin MDD a kasar, Fode Ndiaye ya jinjinawa yunkurin a matsayin wanda zai karfafa fatan shawo kan cutar, yana mai cewa zai kuma taimakawa kokarin hukumomi na yi wa kaso 20 na al’ummar kasar riga kafi. Kasar Senegal kuma ta samu allurai 320,000.

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta karbi sama da allurai miliyan 1.7. A kuma ranar Talata ne Gambia ta karbi kashin farko na alluran riga kafi 36,000 karkashin shirin COVAX.

Bisa taimakon MDD, Angola ta samu sama da allurai 620,000 a ranar Talata, wadanda za su taimakawa kasar yi wa kaso 10 na al’ummarta riga kafin a kashin farko. (Fa’iza Mustapha)