logo

HAUSA

Sakataren MDD ya yi kira da a kare dazuka da namun daji

2021-03-04 10:50:43 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga jama’a, da su kare dazuka da ma halittu daban-daban dake rayuwa a ciki, a matsayinsu na wadanda ke taimakawa rayuwar matalauta da ‘yan asalin mazauna yankuna.

Guterres ya yi wannan kira ne, albarkacin ranar namun daji ta duniya, wadda aka yi bikin ta jiya Laraba 3 ga watan Maris. Taken bikin na bana shi ne. “Dazuka, rayuwa: kare jama’a da duniya baki daya”

Ya ce, kimanin kaso 80 cikin 100 na halittu dake doron duniya, suna rayuwa ne a dazukan dake kewaye da mu. Suna kuma taimakawa wajen daidaita yanayi da yadda daruruwan miliyoyin mutane ke rayuwa.

Jami’in na MDD ya bayyana cewa, akwai kuma wasu kaso 90 ckin 100 na wadanda suka fi kowa talauci a duniya dake rayuwa kan albarkatun gandun daji, musamman ‘yan asalin yankuna dake rayuwa a kusa ko cikin dazukan.

Ya ce, rashin kare wadannan dazuka daga lalata su, yana illa ga wadannan al’ummomi, baya ga haddasa hasarar halittu daban-daban da kuma sauyin yanayi. A ko wace shekara, ana hasarar eka miliyan 4.7 na dazuka, girman filin da ya dara kasar Denmark.

A don haka, albarkacin bikin na bana, yana kira ga gwamnatoci, da ‘yan kasuwa da jama’a ko’ina suke a wannan duniya, da su kara zage damtse wajen kare dazuka da nau’o’in halittun dake rayuwa a cikinsu, su kuma ba da goyon baya tare da sauraron muryoyin al’ummomin dake rayuwa a dazuka. A cewarsa, yin haka zai bayar da gagarumar gudummawa wajen cimma manufofin samun ci gaba mai dorewa ga daukacin jama’a, da duniya gami da makoma.(Ibrahim)