logo

HAUSA

An bayyana nasarar kasar Sin wajen yaki da talauci a matsayin abun misali

2021-03-04 10:36:59 CRI

Mataimakin daraktan shirin raya kasashe na MDD a yankin Latin Amurka da Caribbean, Lenni Montiel, ya ce nasarar kasar Sin na yaki da talauci ya zama abun misali ga aikin kawar da fatara.

Lenni Montiel, ya bayanna haka ne jiya a birnin New York, lokacin da zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi bayani dangane da nasarorin kasarsa a fagen yaki da talauci.

A cewarsa, kasar Sin ta yi namijin kokarin da ba a taba gani ba a tarihi a bangaren yaki da talauci, lamarin da ya bada gagarumar gudunmuwa ga aikin yaki da talauci a duniya.

Ya ce ya gano wasu muhimman batutuwa 3 daga matakan kasar Sin, wadanda za su amfani kasashe masu tasowa. Batutuwan sun hada da: daidaitattun manufofi da tsarukan tattara bayanai na kasa da kuma matakan da aka dauka.

Jami’in na MDD ya bada shawarar yayata matakan kasar Sin na yaki da talauci ga sauran kasashe da kuma ta hanyar inganta hadin kan kasashe masu tasowa, domin tabbatar da cimma ajandar 2030. (Fa’iza Mustapha)