logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a inganta tsarin siyasa a Sudan ta Kudu

2021-03-04 10:53:23 CRI

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a yi kokarin inganta tsarin siyasa a kasar Sudan ta Kudu.

Da yake jawabi ga Kwamitin Sulhu na MDD, Zhang Jun ya ce, a bana ake cika shekaru 10 da kafuwar Sudan ta Kudu. Kuma cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar ta shawo kan kalubale da dama, kuma ta samu sabuwar nasara wajen gina kasa. Ya kara da cewa, yanayin kasar a yanzu, na gabatar da tarin kalubale da kuma damarmaki, a don haka, ya kamata a ci gaba da tabbatar da tsarin siyasa a kasar.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin na karfafa gwiwar dukkan bangarorin dake kasar, su karfafa nasarorin da aka samu da ingiza muhimman ayyukan tsaro da aka tsara da sake fasalin majalisar dokoki da shirya manyan zabuka da ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da kuma warware sabani cikin lumana. (Fa’iza Mustapha)