logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da wasu ingantattun hotunan duniyar Mars daga kumbon bincike na Tianwen-1

2021-03-04 13:58:25 CRI

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin CNSA, ta wallafa wasu ingantattun hotuna 3 na duniyar Mars da kumbon bincike na Tianwen-1 ya dauka.

A cewar hukumar CNSA, hotunan 3, sun hada da marasa kala guda biyu da mai kala guda.

A cikin hotunan, ana iya ganin yanayin kasar duniyar Mars da kananan gulabe da tuddan tsaunika da na kasa a bayyane

Hoton mai kala, na yankin arewacin duniyar ta Mars ne da kyamarar mai matsakaicin inganci ya dauka. (Fa’iza Mustapha)