logo

HAUSA

Kamata ya yi baligai su dauki awoyi 7 zuwa 8 suna barci a kowace rana

2021-09-13 07:34:54 CRI

Kamata ya yi baligai su dauki awoyi 7 zuwa 8 suna barci a kowace rana_fororder_u=1165139991,3554104013&fm=26&fmt=auto&gp=0

Kwanan baya, wasu masu ilmin likitanci na kasar Sin sun ba da shawarar cewa, ya kamata baligai su dauki awoyi 7 zuwa 8 suna barci a kowace rana. Haka kuma ya dace su rika yin abubuwan da suka saba yi ta fuskar yin aiki da hutawa, su kuma kyautata tunaninsu, idan sun gamu da matsalar barci, to, su je ganin likita kan lokaci.

Abubuwan da aka tanada cikin shirin ayyuka na shekarar 2019 zuwa 2030 dangane da kiwon lafiyar mutanen kasar Sin sun nuna cewa, yanzu matsakaicin tsawon lokacin da baligan kasar Sin suke dauka wajen yin barci ya kai awoyi 6.5 a kowace rana. Saboda haka shirin ya fito da manufar kara adadin zuwa awoyi 7 zuwa 8 a kowace rana daga shekarar 2022 zuwa 2030.

Gao Fu, darektan cibiyar kandagarki da dakile cututtuka ta kasar Sin ya yi bayani da cewa, yanzu matsalar barci da cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da matsalar barci suna kara addabar mutanen kasar Sin. Wasu mutane fiye da miliyan 400 suna fama da matsalar barci a nan kasar Sin. Kuma kusan kaso 60 cikin 100 na kananan yara da matasa ne ba sa barci isasshe. Sabon nazari ya nuna cewa, matsalar karancin barci cikin dogon lokaci yana kara barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini, ciwon bakin ciki, ciwon sukari da matsalar kiba, tare da illata kwarewar fahimta, kwarewar tunatar da abubuwa, da tsarin garkuwar jiki. Akwai cututtuka iri-iri fiye da 80 da suke da nasaba da matsalar barci.

Masana sun yi nuni da cewa, akwai shaidu ta fuskar kimiyya dake nuna cewa, dole ne baligai su dauki awoyi 7 zuwa 8 a kowace rana suna barci, lamarin da yake amfanawa lafiyar mutane. Amma sakamakon dalilai da dama, ya sa tsawon lokacin barci yake raguwa ga yawancin mutane. Yawan mutanen da ke fama da matsalolin barci, musamman ma matsalar karancin barci, yana karuwa.

Mene ne dalilin da ya sa haka? Saboda mutane na kara fuskantar babban matsin lambar yin takara mai zafi sakamakon ci gaban tattalin arziki da zamantaker al’ummar kasa. Bayan haka kuma, wasu ba sa rayuwa ta hanyar da ta dace. Alal misali, suna sabawa da yin barci a makare a duhun dare, suna matukar sha’awar yin wasa da wayar salula. Har ila yau  tsufa na tsananta matsalar barci.

Dangane da matsalar barci, madam Zhang Chuji, wata likita dake aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta gaya mana cewa, ana bukatar daidaita matsalar barci baki daya ta hanyar kimiyya. Kowa da kowa na iya kare kansa daga matsalar barci ta hanyar yin rayuwa yadda ya kamata. Amma idan matsalar barci ta yi illa ga ayyukan yau da kullum da zaman rayuwar yau da kullum, to, ya fi kyau a je ganin likita kan lokaci.

Sabili da haka ne gwamnatin Sin ta karfafa gwiwar hukumomin likitanci su ba da hidimar barci, alal misali, ba da jagora kan yin barci ta hanyar kimiyya, a kokarin rage abkuwar matsalar barci ga baligai. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan