logo

HAUSA

Rundunar ‘yan sandan kungiyar kasashen Sahel sun fara atisayen farko a Niamey

2021-09-21 16:36:09 CRI

Jiya ne, sashen ‘yan sanda na kungiyar kasashen Sahel, da ya kunshi sojoji da jandarma da ‘yan sanda da alkalan majistare, daga kasashe mambobin kungiyar biyar, suka fara atisayen yaki da ta’addanci a birnin Niamey na jamhuriyar Nijar.

Rundunar hadin gwiwar kungiyar G5 Sahel dai, ta kunshi sojoji ne daga kasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso da Chadi da Mauritania, an kuma kafa ta ne a shekarar 2017 bisa shawarar shugabannin kasashen biyar, don yaki da karuwar barazanar ayyukan ta’ddanci da rashin tsaro a yankin hamadar Sahara da na Sahel a cikin shekarun baya-bayan nan.

Rundunar ‘yan sandan kungiyar, ta kunshi sassan jandarmomi da kwararru a fannin bincike na kasa da aka tura tare da jami’an sojoji na rundunar hadin gwiwar, ba kawai don ta taimakawa ayyukan rundunar hadin gwiwar ba, har ta tabbatar da cewa, an hukunta wadanda aka kama, kamar yadda sanarwar bayan taron kungiyar ta bayyana.

A cewar wannan majiya, a cikin kwanaki kimanin 10, wato daga ranar 20 zuwa 29 ga watan Satumba, atisayen ya mayar da hankali wajen tsara matakan shari’a a yankin da ake gudanar da aikin hadin gwiwa, da bitar yadda ake gudanar da sashen shari’a na bangaren ‘yan sanda na kungiyar hadin gwiwa a kowace kasa na kasashen Sahel biyar.  (Ibrahim)

Ibrahim