WIPO: Kasar Sin Na Gab Da Shiga Jerin Kasashe 10 Masu Karfin Kirkire-kirkire A Duniya
2021-09-21 16:07:55 CRI
Kasar Sin ce kasa daya tilo mai matsakaicin kudin shiga, da ke cikin jerin kasashe 30 dake kan gaba a fannin kirkire-kirkire a duniya, inda take neman zama jagora a wannan fanni, tare da neman shiga cikin kasashe 10 dake kan gaba.
Rahoton alkaluman GII da hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta duniya WIPO ta fitar, ya nuna cewa, kasar Sin na ci gaba da samun nasara, daga kasancewa a matsayi na 14 a bara, zuwa na 12 a bana, inda yanzu take neman shiga cikin kasashe 10 na farko, lamarin dake jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da dabaru da matakan gwamnati na kara azama kan kirkire-kirkire.
A cewar alkaluman GII dake auna matsayin kasashe a fannin kirkire-kirkire a duniya, adadin shaidar hakkin mallakar fasaha na kasar Sin, wanda aka auna bisa alkaluman GDP, ya zarce na kasashen Japan da Jamus da Amurka. Kuma haka batun yake a fannin tambura da fasalin masana’antu.
Alkaluman na GII da a kan wallafa a kowacce shekara, na auna kwazo tare da zayyana matsayin kasashe 132 a fannin kirkire-kirkire. A shekarun da suka gabata, kasashen Switzerland da Sweden da Amurka da Birtaniya ne ke ci gaba da jagorantar jerin kasashen. (Fa’iza Mustapha)
Labarai Masu Nasaba
- Wakilin Sin: Doka Da Odar Kasa Da Kasa Cikin Adalci Da Demokuradiya Na Da Muhimmanci Wajen Kare Hakkin Bil-Adama
- Sin na goyon bayan hanyar da kasar Rasha ta zaba
- Xi ya aike da sakon ta’aziyya bisa mutuwar tsohon shugaban Algeria Bouteflika
- CMG zai kasance kafar watsa labaru daya tilo da zai yi amfani da Sinanci wajen watsa labaru game da bikin baje kolin duniya na Dubai