logo

HAUSA

Adadin wadanda cutar cholera ta hallaka a Najeriya ya karu zuwa 2,404

2021-09-22 10:16:39 CRI

Adadin wadanda cutar cholera ta hallaka a Najeriya ya karu zuwa 2,404_fororder_210922-Nigeria's cholera-Saminu1

Cibiyar yaki da cututtuka ta tarayyar Najeriya NCDC, ta ce daga watan Janairu zuwa yanzu, adadin mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon harbuwa da cutar amai da gudawa ko cholera a sassan kasar, ya karu zuwa mutum 2,404.

Cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar a jiya Talata, NCDCn ta ce tsakanin ranekun 6 zuwa 12 ga watan nan na Satumba, an samu sabbin mutane 23 da suka rasu sanadiyyar barkewar annobar. Kaza lika tsakanin wannan lokaci, an samu karin sabbin mutane 1,182 da ake zaton su ma sun harbu.

Sanarwar ta kara da cewa bisa jimilla, ana zaton mutane 72,910 sun harbu da cutar a jihohin kasar 27, da kuma birnin Abuja fadar mulkin kasar.

NCDC ta ce tuni aka tsara wani shirin hadin gwiwar sassan masu ruwa da tsaki na kasa baki daya, domin gaggauta aiwatar da matakan shawo kan wannan annoba.   (Saminu)