logo

HAUSA

Guterres ya gargadi kasashen duniya yayin da za a bude muhawarar babban zauren majalisar

2021-09-22 11:06:43 CRI

Guterres ya gargadi kasashen duniya yayin da za a bude muhawarar babban zauren majalisar_fororder_210922-UN-Faeza1

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci al’ummomin duniya su warware matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya yayin da duniya ke fama da annobar COVID-19.

Da yake jawabi ga zauren kafin bude muhawarar, Antonio Guterres ya ce yana mai gargadin dole duniya ta farka. Inda ya ce ana gab da shiga wani matsanancin yanayi, yayin da ake tafiya kan wata bahaguwar hanya.

A cewarsa, ba a taba ganin barazana ko rarrabuwar kawuna da ake gani a yanzu ba, inda ake fama da tarin matsaloli. Yana mai bada misali da batutuwan da suka hada da rashin daidaito a fannin yaki da COVID-19 da tashin hankali a Afghanistan da Habasha da Yemen, da suka kawo nakasu ga zaman lafiya da karuwar rashin yadda bayanan bogi dake rarraba mutane da al’ummomi da keta hakkin dan adam da yadda ake farwa kimiyya da jinkiri ko karancin tallafin kudi ga masu rauni da kuma rashin hadin kai. (Fa’iza Mustapha)