logo

HAUSA

MDD ta samar da tallafin gaggawa ga jamhuriyar Nijar

2021-09-22 10:27:41 CRI

MDD ta samar da tallafin gaggawa ga jamhuriyar Nijar_fororder_210922-Nijer-Saminu2

MDD ta samar da tallafin gaggawa na kudi har dalar Amurka miliyan 8.5 ga jamhuriyar Nijar, a wani mataki na baiwa kasar damar inganta rayuwar wadanda tashin hankali ya raba da yankunansu a cikin kasar, da kalubalen ambaliyar ruwa, da cutar amai da gudawa.

Sakataren kula da ayyukan jin kai na MDDr Martin Griffiths ne ya ba da umarnin sakin kudaden a ranar Litinin, domin kasar ta samu zarafin karfafa fannin kiwon lafiyar ta, da samar da ruwan sha mai tsafta, da tsaftar muhalli, da samar da matsugunai, da ababen masarufi, da tsaro da tallafin ilimi ga sama da ’yan Nijar 720,000.

Ofishin lura da ayyukan jin kai na MDD OCHA, ya ce kudaden da aka baiwa kasar tallafi, za su taimaka wajen farfado da rayuwar rukunin mutane masu rauni sama da 81,600, wadanda suka kunshi sabbin wadanda aka raba da muhallansu, da masu komawa yankunansu na asali bayan fuskantar tashen rashin hankula a yankunan Diffa, da Maradi, da Tahoua da Tillaberi.

Ana sa ran hukumar kasa da kasa mai lura da harkokin bakin haure, da WHO, da asusun yara na MDD, da sauran abokan huldar su ne za su aiwatar da shirin.

Jamhuriyar Nijar na da sama da masu fama da cutar amai da gudawa 4,600, ciki har da mutum 149 da cutar ta hallaka, yayin da kuma ambaliyar ruwa ta shafi kusan mutane 200,000.  (Saminu)