logo

HAUSA

Sin Da Najeriya Sun Kaddamar Da Makon Al’adu Yayin Da Kasashen Ke Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diflomasiya

2021-09-22 19:14:47 CRI

Jiya ne, kasashen Sin da Najeriya suka kaddamar da makon al’adu, da nufin karfafa dadadden zumuncin dake tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

Da yake jawabi a wajen bikin, Jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya bayyana cewa, bikin na musamman ne, wanda kuma ya dace yayin da a bana kasashen ke cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu. Cui ya bayyana yayin bikin da ya samu halartar jami’an Najeriya, da ‘yan jaridu da ma’aikatan wurin dake aiki a kamfanonin kasar Sin da sauransu cewa, Najeriya da Sin manyan kasashe ne dake da dadadden tarihi da al’adu masu kyau. Yana mai cewa, za a kara inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare da karfafa zumuncin gargajiya ta hanyar hadin gwiwar makon al’adun kasashen biyu wato Sin da Najeriya.

Makon al’adun ya kunshi nune-nunen al’adun Sinawa da na Najeriya, da gasar daukar hotuna da gajerun bidiyo da fasahar rubutu na kasar Sin da fina-finai dake nuna sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, babban sakatare a ma’aikatar watsa labaru da al’adu ta Najeriya Adaora Anyanwutaku ya ce, makon al’adun yana ba da shaida ba kawai dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da jama’arsu ba, har ma da nasarar hadin gwiwar al’adunsu.(Ibrahim)

Ibrahim