logo

HAUSA

Galibin ’yan Afrika na fargabar riga kafin COVID-19 yayin da ake yada bayanan bogi

2021-09-22 11:11:58 CRI

Galibin ’yan Afrika na fargabar riga kafin COVID-19 yayin da ake yada bayanan bogi_fororder_210922-AU-Faeza2

Tarayyar Afrika AU, ta ce bayanan bogin dake wadari game da riga kafin COVID-19, sun sa galibin mutane a fadin Afrika sun nuna shakku game da alluran.

Wata sanarwar da William Carew, shugaban majalisar kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewa da al’adu na majalisar ya fitar, ya bukaci al’ummar nahiyar su karbi allurar idan har ana son samun tarin mutanen dake da karfin garkuwar jiki. Yana mai cewa kawo yanzu, kaso 3.6 na al’ummar nahiyar ne kadai suka karbi riga kafin.

A makon da ya gabata ne hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce an tilastawa shirin COVAX rage yawan alluran da aka tsara zai samar ga nahiyar a bana, da kusan miliyan 150.

Da wannan ragin da aka samu, yanzu ana sa ran COVAX din zai samar da allurai miliyan 470 a bana, wanda zai wadaci kaso 17 na al’ummar, adadin da ya yi kasa sosai da kaso 40 da ake burin cimmawa.

Bisa sabon alkaluman da cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika ta fitar, zuwa jiya Talata, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a nahiyar ya kai 8,166,634, yayin da yawan mamata ya kai 206,740. (Fa’iza Mustapha)