logo

HAUSA

Sin: Ana fatan kasashen da abin ya shafa za su tafi da zamani

2021-09-23 09:59:24 CRI

Sin: Ana fatan kasashen da abin ya shafa za su tafi da zamani_fororder_趙立堅-3

Shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana a gun taron muhawara na babban taron MDD da aka kira a ranar 21 ga wannan wata cewa, kasarsa ba ta son cacar baka. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya mayar da martani yayin taron ganawa da manema labarai da aka shirya jiya Laraba 22 ga wata, inda ya yi tsokaci da cewa, ana fatan kasashen da batun ya shafa za su tafi da zamani, haka kuma su daidaita huldar dake tsakaninsu da kasar Sin yadda ya kamata, kana su amince da ci gaban kasar Sin, da hankali da kuma hangen nesa. Jami’in ya jaddada cewa, samun ci gaba cikin lumana, da samun moriya tare cikin hadin gwiwa buri ne na kasa da kasa. Yana mai cewa,“Bai dace a daidaita harkokin kasa da kasa bisa matsayin karfin kasashe ba, kuma bai kamata a gurgunta tsarin duniya bisa fakewa da ka’idoji ba, ya dace a nace kan manufar hadin gwiwa bisa tushen samun moriya tare.”

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, a ko da yaushe, kasar Sin mai gina zaman lafiya ce, wadda kuma ke taka rawa wajen raya kasashen duniya, mai kiyaye tsarin duniya, wadda za ta ci gaba da samar da sabbin damammaki ga sauran kasashen duniya.  (Jamila)