logo

HAUSA

Jiang Duan: Ya kamata a daina daukar matakan soja ba bisa ka’ida ba game da hakkin dan adam

2021-09-23 10:58:49 CRI

Jiang Duan: Ya kamata a daina daukar matakan soja ba bisa ka’ida ba game da hakkin dan adam_fororder_0923A1-hakkinBilAdama

Kasar Sin da gamayyar kasashen da abin ya shafa sun bukaci kwamitin kare hakkin bil adama na MDD, da kwamishinan hukumar kare hakkin dan adam da sauran matakan musamman na MDD da su maida hankali game da illolin dake tattare da amfani da daukin sojoji ba bisa ka’ida ba wanda ke shafar hakkin dan adam, kana ya kamata su dauki dukkan matakan da suka dace wajen kwatowa mutane hakkokinsu a kasashen da aka ci zarafinsu.

Da yake jawabi a madadin kasashen da abin ya shafa a taron kolin kwamitin kare hakkin bil adama na MDD karo 48, Jiang Duan, ministan ofishin jakadancin kasar Sin a MDD dake Geneva, ya ce, kasashen da aka kaddamar da dauki soji ba bisa ka’ida ba da kuma dogon lokacin da dakarun kasashen waje suka shafe wajen mamaye kasashen nasu, wanda hakan ya yi matukar saba dokokin kasa da kasa, kana ya lahanta ikon kasashen da aka keta musu haddi wajen tafiyar da ikon mulkin yankunansu.

Jakadan na Sin ya bukaci kasashen da abin ya shafa da su gaggauta dena jibge sojojinsu a matsayin kai daukin soji ba bisa ka’ida ba, sannan su biya diyya ga kasashen da aka ketawa haddin. (Ahmad)