logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da shugaban babban zaman MDD karo na 76

2021-09-24 15:45:59 CRI

Wang Yi ya gana da shugaban babban zaman MDD karo na 76_fororder_210924-Saminu4-Wang Yi

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da shugaban babban zaman MDD karo na 76 Abdulla Shahid ta kafar bidiyo.

Yayin zantawarsu a jiya Alhamis, Mr. Wang ya yi kira ga babban zauren MDDr da ya taka babbar rawa, wajen ingiza hadin gwiwar yaki da annobar COVID-19, da tabbatar da daidaito wajen rabon alluran rigakafin cutar, da tallafawa kyautata ayyukan dakile sauyin yanayi, da inganta sarrafa sinadarai daga kwayoyin halittu, da bunkasa samar da ci gaba mai dorewa.

Mr. Wang ya ce, a bana ake cikin shekaru 50 tun bayan da Sin ta sake karbar kujerarta ta MDD bisa doka, kuma Sin za ta ci gaba da jefa kuri’un ta ga bukatun kasashe masu tasowa, za ta kuma ci gaba da tallafawa manufofin adalci da daidaito a matakin kasa da kasa.

A nasa bangare kuwa, Mr. Shahid ya mika sakon murnar cika shekaru 100 ne da kafuwar JKS, da murnar cika shekaru 50 da mayarwa Sin kujerar ta ta MDD, yana mai bayyana fatan ci gaba da aiki kafada da kafada da Sin a dukkanin muhimman ayyukan dake kunshe cikin ajandojin babban taron MDD.

Daga nan dan sai ya yiwa Sin fatan cimma nasarar gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu dake tafe a badi lami lafiya.(Saminu Hassan)