logo

HAUSA

Xi ya tattauna ta wayar tarho da babban sakataren tsakiyar kwaminis na kasar Vietnam da Tonga's King Tupou VI da firaministan Solomon Islands

2021-09-24 15:46:54 CRI

Babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, a yau Juma’a ya bayyana cewa a yanzu ana cikin wani muhimmin lokaci na bukatar inganta kyautata huldar dake tsakanin Sin da Vietnam domin kiyaye tsaron gwamnatocin kasashen karkashin jam’iyyun kwaminis da kuma tsarinsu na gurguzu.

Xi ya yi wannan tsokaci ne a yayin tattaunawarsa ta wayar tarho tare da babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis na kasar Vietnam, Nguyen Phu Trong.

A zantawa ta wayar tarho da sarkin Tonga, Tupou VI, Xi ya kuma bayyana cewa kasar Sin za ta samar da taimakon kudade da fasahohi ga Tonga ba tare da gindaya sharadin siyasa ba.

A zantawarsa ta wayar tarho da Manasseh Sogavare, firaministan tsibirin Solomon Islands, shugaba Xi ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi musayar kwarewar da ta samu a fannonin yaki da talauci da zurfafa hadin gwiwar raya ci gaban kasa da tsibirin Solomon Islands da sauran tsibirrai dake kasashen yankin Pacific. (Ahmad Hassan)