logo

HAUSA

Ana share fagen bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na 2

2021-09-24 10:08:45 CRI

Ana share fagen bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na 2_fororder_biki

Za a gudanar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na biyu a Changsha, fadar mulkin lardin Hunan dake kudancin kasar Sin, tsakanin ranekun 26 zuwa 29 ga wannan watan da muke ciki, a zahiri ko kuma ta yanar gizo, inda za a shirya ayyuka 23. An kuma tsaya cewa, kasashen Aljeriya, da Habasha, da Kenya, da Ruwanda, da Afirka ta kudu, da Senegal za su kasance manyan baki, yayin da Zhejiang da Jiangxi za su kasance manyan larduna.

Abun farin ciki shi ne, za a daddale wasu sabbin kwangilolin ayyukan hadin gwiwa, tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da dama yayin bikin, kuma za a fitar da wasu sabbin sakamakon da sassan biyu suka samu a hukumance, wadanda suke kumshe da “Kundin dabarun hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka”, da “rahoton huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Afirka”.

Kawo yanzu, an riga an tattara ayyukan hadin gwiwa 554 masu darajar dalar Amurka biliyan 15.93, da biranen lardunan kasar Sin, da manyan kamfanonin kasar, da ofisoshin jakadancin kasashen Afirka dake kasar Sin suka gabatar.  (Jamila)