logo

HAUSA

A karon farko masana kimiyya na Sin sun samar da sitati daga iskar carbon dioxide

2021-09-24 10:22:14 CRI

A karon farko masana kimiyya na Sin sun samar da sitati daga iskar carbon dioxide_fororder_210924-Saminu2-sitati

A karon farko a tarihin duniya, wasu masana kimiyya na kasar Sin sun samar da sinadarin sitati daga iskar carbon dioxide.

Cibiyar bincike a fannin sarrafa kwayoyin halittu masu rai ta Tianjin, dake karkashin cibiyar masana kimiyya ta Sin ce ta gabatar da rahoton binciken, aka kuma wallafa shi kan mujallar kimiyya ta yanar gizo a Juma’ar nan.  (Saminu)