logo

HAUSA

An bude baje kolin ICIF karo na 17 a birnin Shenzhen na kasar Sin

2021-09-24 11:19:07 CRI

An bude baje kolin ICIF karo na 17 a birnin Shenzhen na kasar Sin_fororder_210924-Saminu3-ICIF

An bude baje kolin kasa da kasa, na tallata sassan masana’antun raya al’adu ko ICIF, karo na 17 a birnin Shenzhen na kasar Sin.

Taron wanda ya fara gudana tun daga jiya Alhamis, ya hallara jimillar tawagogin gwamnatocin kasashe daban daban har 2,468, da wakilan cibiyoyi da kamfanonin raya al’adu, da masu baje koli 868, da kuma masu sana’o’in raya al’adu dake baje hajojinsu ta yanar gizo.

Mashirya bajen kolin na ICIF sun ce, a duk shekara, ana baje hajojin da suka shafi masana’antun kirkire-kirkire na raya al’adu da cinikayya a gida da waje sama da 100,000, wanda hakan ya sanya kasar Sin zama jagora a fannin kirkire kirkire, da samar da ci gaba ga sha’anin raya al’adu.  (Saminu)