logo

HAUSA

Sin: Fitar da takardun tsoma baki cikin harkokin HK, mayar da martani ne ga Amurka

2021-09-24 15:28:16 CRI

Sin: Fitar da takardun tsoma baki cikin harkokin HK, mayar da martani ne ga Amurka_fororder_HK

Yau Jumma’a, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da bayani mai lakabin “Takardun tsoma baki a cikin harkokin yankin Hong Kong na kasar Sin, da nuna goyon baya ga masu tayar da tarzoma a yankin da kasar Amurka take yi”.

Kakakin ofishin ma’aikatar harkokin wajen kasar dake yankin ya bayyana cewa, makasudin fitar da takardun shi ne mayar da martani ga matakan da Amurka ta dauka a kwanakin baya, wato ta yi kashedi kan kasuwancin Hong Kong, da sanya takunkumi kan jami’an hukumomin kwamitin tsakiya na JKS dake yankin Hong Kong, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana nacewa kan manufarta ta kare ikon mulki, da kwanciyar hankali da moriyar ci gaba. Haka kuma matakin ya nuna cewa, kasar Sin tana nacewa kan manufar kiyaye zaman lafiya da wadata a yankin Hong Kong.

Kakakin ofishin Hong Kong da Macao, na majalissar gudanarwar kasar Sin, shi ma ya yi sharhi kan batun fitar da takardun, inda ya nuna goyon baya ga lamarin.  (Jamila)