logo

HAUSA

Afirka na bukatar karin ninki 7 na riga-kafin COVID-19

2021-09-24 10:14:21 CRI

Afirka na bukatar karin ninki 7 na riga-kafin COVID-19_fororder_210924-Ahmad1-vaccine

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, tilas ne a samu ninki bakwai na adadin alluran riga-kafin COVID-19 ga Afrika wato daga miliyan 20 zuwa miliyan 150 a kowane wata idan har ana son yiwa kashi 70 bisa 100 na mutanen nahiyar riga-kafin nan da watan Satumbar shekarar 2022.

An cimma matsayar neman yiwa kashi 70 bisa dari na mutanen Afrikan riga-kafin ne a yayin taron kolin duniya game da annobar COVID-19 a gefen taron kolin MDD a wannan mako.

Ana cigaba da shigar da riga-kafin zuwa kasashen Afrika karkashin shirin samarwa da rarraba riga-kafin na COVAX, inda a makon jiya an kai allurai miliyan 4 zuwa nahiyar. To sai dai kuma, har yanzu kashi uku kacal aka samar na riga-kafin da kasashe masu arziki suka yi alkawarin samarwa Afrika zuwa karshen shekarar 2021.

Dr. Matshidiso Moeti, daraktan hukumar WHO na shiyyar Afrika ya ce, ya kamata a tabbatar da wannan aniya a aikace maimakon kalaman fatar baki, sannan kasashen Afrika suna bukatar a fayyace takamammun ranakun shigar musu da riga-kafin domin su samu damar kimtsaya yadda ya kamata.

Hukumar WHO ta yi gargadin cewa, wani bincike ya gano cewa, tabbatar tsaro wajen samar da riga-kafin da kuma rashin tabbas game da rarraba shi na daga cikin manyan kalubalolin dake damun kasashe da dama a Afrika. (Ahmad Fagam)