logo

HAUSA

Wakiliyar CNN: Daya daga cikin Amurkawa biyar sun kamu da Covid-19

2022-01-20 14:34:15 CRI

Wakiliyar CNN: Daya daga cikin Amurkawa biyar sun kamu da Covid-19_fororder_220120-A4-推送

Jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka ta bayyana cewa, yanzu haka, a kalla kashi 20 cikin 100 na Amurkawa sun kamu da cutar ta Covid-19 a tsawon lokacin barkewar cutar.

A cewar bayanan jami’ar ta John Hopkins (JHU), a kalla mutane 66,356,336 aka gano sun kamu da cutar Covid-19 a tsawon lokacin barkewarta a Amurka, kana fiye da mutane 800,000 ne suka mutu.

Bugu da kari, matsakaicin sabbin masu kamuwa da cutar a Amurka, sun kai mutane 777,453 baya ga sabbin mutane 1,797 dake mutuwa sanadiyar cutar a kowace rana.

Dr. Vivek Murthy dake kasar ta Amurka, ya fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa, yanayin yaduwar nau’in cutar COVID-19 na Omicron a cikin kasar ba daya ba ne.

Murthy ya ce, yayin da yawan masu kamuwa da cutar ke kara yaduwa, da kuma raguwa a wasu yankuna, bai kamata Amurkawa su yi tsammanin kololuwar yaduwar cutar a kasar da wuri ba, kuma yanayin yaduwar cutar, zai kazanta a cikin ’yan makonni masu zuwa. (Ibrahim Yaya)