logo

HAUSA

Masana'antar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi ta shiga sabon matakin ci gaba

2022-01-21 09:53:13 CRI

Masana'antar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi ta shiga sabon matakin ci gaba_fororder_0121-i02-New energe

Ma'aikatar masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, masana'antar kera motoci masu amfani da sabbin mamakashi ta kasar Sin, ta shiga wani sabon mataki na saurin bunkasuwa tare da ci gaba da inganta tsarin samar da kayayyaki na masana'antu.

Alkaluman da ma’aikatar ta fitar jiya Alhamis sun nuna cewa, yadda ake samarwa da sayar da motoci masu amfani da sabbin makamashi a kasar Sin, kowacce ta karu da kashi 160 cikin 100 a duk shekara, wanda ya zarce motoci miliyan 3.5 a bara.

Bayanai na nuna cewa, yadda ake inganta matakan samar da kayayyaki more rayuwa, ya kara fadada kasuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi. 

Luo Junjie, jami'in ma'aikatar ya ce, bisa hadin gwiwar gwamnatoci a dukkan matakai da kamfanonin kera motoci da irin wadannan na’urori, an samu saukin tasirin karancin na’urar dake tattara bayanai da motacin ke amfani da su a shekarar 2021. Yana mai cewa, ma'aikatar za ta ci gaba da kara kaimi, wajen ba da tabbacin samar da na'urorin kera motoci da inganta karfin yadda ake samar da irin wadannan kananan na’urori. (Ibrahim Yaya)