logo

HAUSA

Sin: Amurka ta yi rashin adalci game da batun sayarwa Australia makamai masu linzami

2022-01-21 19:13:22 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya soki matakin Amurka, na shirin kakabawa wasu kamfanonin Sin 3 takunkumi, bayan da ta zarge su da yada fasahohin makamai masu linzami.

Zhao Lijian, wanda ya yi wannan suka a Juma’ar nan, ya ce ko shakka babu, Amurka ta dauki matakin nuna fin karfi, duba da yadda ita da kan ta, ke shirin sayarwa kasar Australia roka mai linzami dake iya gudun kilomita 2,500, wadda kuma ke iya daukar makamin nukiliya.

Zhao ya ce har kullum kasar Sin na adawa da yaduwar makaman kare dangi da musayar su, kuma Sin na da ka’idoji masu tsauri na fitar da makamai masu linzami, da sauran fasahohi masu alaka da su.

Jami’in ya kara da cewa, Amurka ta dau matsaya 2 game da wannan batu, inda a hannu guda, take goyon bayan kawayen ta wajen samar da irin wadannan makamai, da sauran fasahohi masu alaka da su, har ma a yanzu take shirin sayarwa Australia makamin Tomahawk. A hannu guda kuma, ta ayyana sanyawa kamfanonin Sin masu nasaba da wannan batu takunkumi.

Daga nan sai Zhao ya yi kira ga Amurka, da ta gaggauta gyara kurakuran ta, ta janye takunkuman da take shirin sanyawa kamfanonin Sin, kana ta dakatar da yunkurin danne kamfanonin Sin, da shafawa Sin din kashin kaji.    (Saminu)