logo

HAUSA

Shugaban taron kolin MDD ya bukaci a martaba yarjejeniyar zaman lafiya ta Olympic a lokacin wasannin motsa jiki na Beijing 2022

2022-01-21 11:20:37 CRI

Shugaban taron kolin MDD ya bukaci a martaba yarjejeniyar zaman lafiya ta Olympic a lokacin wasannin motsa jiki na Beijing 2022_fororder_0121-a02

Shugaban babban taron MDD Abdulla Shahid, a ranar Alhamis ya yi kira da babbar murya, inda ya bukaci a martaba yarjejeniyar zaman lafiya ta Olympic a lokacin wasannin motsa jiki na lokacin hunturu da wasan ajin nakasassu wanda zai gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shahid ya bayyanawa babban taron MDDr inda ya bukaci dukkan bangarorin da ba sa ga maciji da juna, da kungiyoyi masu dauke da makamai a sassan duniya, da su amince da yarjejeniyar tsakaita bude wuta ta gaskiya a lokacin fara aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar ta Olympic, wadda ta kasance a matsayin wata muhimmiyar dama ta warware dakaddama da samun zaman lafiya mai dorewa.

A watan jiya ne babban taron MDDr ya amince da kudurin doka, inda ya bukaci kasashen mambobin MDD da su sa lura kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Olympic a tsawon kwanaki bakwai gabannin fara wasannin Olympic na lokacin hunturu na Beijing har zuwa kwanaki bakwai na bayan kammala gasar ajin nakasassu.

Kakakin ofishin shugaban babban taron MDDr karo na 76, ya sanar a ranar 20 ga watan Janairu cewa, Shahid zai halarci bikin bude gasar wasannin motsa jikin ta lokacin hunturu ta Beijing, zai kuma halarci bikin kunna fitilar fara wasannin bisa goron gayyatar da kwamitin shirya wasannin Olympic na kasa sa kasa (IOC) yayi masa. (Ahmad Fagam)