logo

HAUSA

An yi bitar farko na liyafar Bikin Bazara na 2022

2022-01-22 16:50:48 CRI

An yi bitar farko na liyafar Bikin Bazara na 2022_fororder_biki

Rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya gudanar da bitar farko na liyafar Bikin Bazara na shekarar 2022 a jiya Juma’a. Bisa taken farin ciki da fatan alkhairi, bikin ya nuna fasahar neman ci gaba da kirkire-kirkiren kimiyya.

Kallon liyafar ta Bikin Bazara ko kuma Chunwan da Sinanci, wani bangare ne dake kunshe da murnar bikin ga Sinawa dake alamta shiga sabuwar shekara.

Liyafar dake karatowa, za ta haska yanayin kasar cikin shekarar da ta gabata, da samar da wani yanayi na farin ciki da murna ta hanyar shirye-shirye da dama. Wasu daga cikin shirye-shiryen sun samo asali ne daga al’adun gargajiya na kasar Sin, yayin da sauran aka kirkiro su daga rayuwar yau da kullum.

Haka kuma za a yi amfani da ingantattun fasahohin zamani cikin shirye-shiryen, ciki har da na XR da VR. Baya ga majigi mai zagaye digiri 720 da aka kafa musammam saboda nuna shirin na bana domin nishadantar da masu kallo.

Za a watsa liyafar ne da karfe 8 na dare, agogon Beijing a ranar 31 ga watan nan na Junairu, wato jajibirin sabuwar shekarar Sinawa.

An fara watsa shirin na sa’o’i 4 ne a shekarar 1983, inda ake daukarsa a matsayin wanda ya fi samun ‘yan kallo a duniya, dake kunshe da shirye-shirye da suka hada da wake-wake da raye-raye da wasannin barkwanci da na kasada da siddabaru da sauransu. (Fa’iza Mustapha)