logo

HAUSA

MDD ta gabatar da takardar hatimi ta sabuwar shekarar Sinawa

2022-01-22 16:26:25 CRI

MDD ta gabatar da takardar hatimi ta sabuwar shekarar Sinawa_fororder_hatimi

Hukumar aikewa da sakonni ta MDD wato UNPA, ta gabatar da takardar hatimi na musammam domin murnar sabuwar shekarar Sinawa.

Takardar na dauke da hatimai 10 kan kudi dala 1.30 kowanne, wadda ke dauke da tambarin MDD a hannun hagu, da kuma hoton damisa cikin furanni a bangaren hannun dama, bisa la’akari da cewa, shekarar 2022, shekara ce ta Damisa bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.

Za a iya sauya fasalin takardar ta hanyar maye gurbin tambarin MDD da hotuna.

Hukumar UNPA ta kammala jerin dabbobin 12 dake alamta shekarar gargajiya ta kasar Sin a bara. Sabon hatimin na Damisa, mafari ne na sabon zagayen kalandar shekarar gargajiya ta kasar Sin cikin jerin hatimanta.

Sabuwar shekarar Sinawa ko Bikin Bazara, biki ne mafi muhimmanci ga Sinawa a fadin duniya, wanda a bana ya fado a ranar 1 ga watan Fabreru. (Fa’iza Mustapha)