logo

HAUSA

Shugabar Tanzania ta kaddamar da bikin raya al’adun gargajiya na shiyyar arewacin kasar

2022-01-23 17:07:27 CRI

Shugabar Tanzania ta kaddamar da bikin raya al’adun gargajiya na shiyyar arewacin kasar_fororder_微信圖片_20220123170709

Shugabar kasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, a karon farko ta kaddamar da bikin wasannin raya al’adun gargajiya na shiyyar arewacin kasar wanda ya kumshi yankin Kilimanjaro, da Arusha, da Manyara da kuma Tanga, inda tayi kira da a tabbatar da kare al’adun gargajiyar kasar.

Yayin kaddamar da bikin, Samia Hassan tace, bukukuwan gargajiyar zasu taimaka wajen zaburar da al’umma muhimmancin al’adunsu, da kuma cusawa matasa sha’awar al’adunsu har zuwa zuriyoyi masu zuwa a nan gaba.

Bikin ya samu halartar manyan yarukan kasar uku daga yankunan Kilimanjaro, Arusha, Manyara da Tanga tare da baje kolin abincin gargajiya da raye-rayen gargajiya. Samia Hassan ta bukaci sauran shiyyoyin kasar da su yi koyi.

A cewar shugabar, kasar Tanzania tana alfahari da al’adunta wadanda aka gaje su daga kabilun kasar 120, ta kara da cewa, wadannan al’adu suna taka muhimmiyar rawa wajen hada kan al’ummar kasar.

Ta kuma yi alkawarin kara yawan kasafin kudi ga ma’aikatar al’adu da wasanni don ta samu damar daga matsayi da kuma kiyaye al’adun gargajiyar kasar.(Ahmad)